Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-03 21:27:18    
Ganawa a tsakanin shugabannin kasashen Sin da Korea ta kudu

cri

Ran 3 ga wata a birnin London, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da Mr. Lee Myung bak takwaransa na kasar Korea ta kudu.

Yayin da ake yin ganawa, Mr. Hu Jintao ya yabawa bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Korea ta kudu. Ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana kula da huldar da ke tsakaninsu sosai, tana son yin kokari tare da kasar Korea ta kudu wajen taimakawar juna bisa cude ni in cude ka, da kara samu damar yin hadin gwiwa, da zurfafa hadin kai a zahiri daga fannoni daban daban, ta haka domin sa kaimi ga bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu.

Mr. Hu ya ce, ya zuwa yanzu, matsalar hada-hadar kudi ta kasa da kasa tana yaduwa, ya kamata kasashen biyu su gano damar warware matsala. Mr. Hu ya ba da kwarin gwiwa ga kamfannonin kasashen biyu da su samar da karfinsu domin kara yin hadin gwiwa domin raya tattalin arzikinsu yadda ya kamata, saboda wannan yana da muhimmiyar ma'ana ga bunkasuwar tattalin arzikinsu har ma na kasashen duniya. Ban da haka kuma, yana fatan hukumomin tattalin arziki na kasashen biyu su kara yin musaya.

Mr. Lee Myung bak ya ce, kokarin da kasar Sin ta yi ya dace da bunkasuwar kasar Sin da kanta, kuma yana da muhimmanci sosai ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Yana fatan za a cigaba da yin hadin gwiwa a gabashin Asiya domin tinkarar matsalar hada-hadar kudi.