Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-03 08:34:50    
Kasashen duniya sun nuna maraba ga sakamakon da aka samu a gun taron G20

cri

An rufe taron koli na kasashe 20 a kan sha'anin kudi a ran 2 ga wata. Majalisar Dinkin Duniya, da hukumar ba da lamuni ta duniya, da kasashen Amirka, Indiya, da Faransa sun nuna gamsuwa ga sakamakon da aka samu a gun taron, kuma sun nuna maraba ga kudurin da aka yi na zuba karin jari ga bankin duniya da hukumar IMF.

Bayan taron, babban sakataren M.D.D. ya ba da sanarwar nuna maraba ga shirin tallafin tattalin arziki na dala biliyan 1100 da shugabannin kasashe 20 suka amince. Ya jaddada cewa, tabbatar da shiri na tallafawa kasashen dake fama da talauci ya fi muhimmanci. Ban da wannan kuma, Ban Ki-moon ya nuna maraba ga alkawarin da aka yi na adawa da matakin kariya da ake dauka wajen yin ciniki.

Babban mataimakin shugaban hukumar IMF John Lipsky ya bayyana cewa, aikin yin gyare-gyare da na zuba jari zai kara karfin hukumar na tinkarar matsalar kudi.

A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi bayan taron, shugaban Amirka Barack Obama ya ce, dole ne kungiyar kasashe 20 ta dauki tsauraran matakan taimakawa kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen da suka fi fama da talauci. Ban da wannan kuma, ya sake nanata muhimmanci na adawa da ra'ayin kariya na yin ciniki.

Firayim ministan kasar Indiya Manmohan Singh ya bayyana cewa, alkawarin da shugabannin kasashe 20 suka yi na samar da dala biliyan 1100 ga hukumomin kudi na duniya shi ne sakamako mai ma'ana da aka samu a gun taron.

Bayan taron, shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba a kan duk batutuwa a gun taron, kuma sakamakon da aka samu ya wuce tsammani. Ya nuna cewa, shugabannin sun yanke shawarar kara yin gyare-gyaren tsarin hukumomin duniya, wannan mataki ya fi muhimmanci tun daga aka tsara tsarin Bretton Woods a shuekaru 40 na karnin da ya gabata.(Asabe)