Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-01 21:35:57    
Ana fatan a samu sakamakon da ake bukata a gun taron koli na G20

cri

A daidai lokacin karatowar taron koli na shugabannin kasashe 20, mambobin kungiyar G20 da za a yi a ran 2 ga wata a London, shugabannin wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sun bayyana bi da bi cewar, suna fatan za a iya samun sakamako a yayin taron domin sassauta rikicin kudi na duniya da kuma bayar da gudummawa wajen kafa wani tsarin sha'anin kudi cikin daidaito kuma cikin adalci.

A ran 1 ga wata, shugaba Barack Obama na kasar Amurka ya bayyana a London, cewar makasudin isarsa a gun taron koli na kungiyar kasashe 20 shi ne bayyana matsayin da kasar Amurka take da shi, kuma yana son saurarar ra'ayoyin sauran kasashen duniya. Mr. Obama ya yi imani cewa, bangarori daban daban dake halartar wannan taro za su iya kawar da bambanci da neman ra'ayi na bai daya, daga karshe dai za su iya samun ra'ayi daya daga dukkan fannoni.

Haka kuma, Mr. Nicolas Sarkozy, shugaban kasar Faransa ya ce, ya kamata a tsara manufofi dalla dalla kan yadda za a sa ido kan kasuwannin kudi na duniya a yayin taron koli na batun sha'anin kudi na kungiyar kasashe 20, bai kamata a daddale wata yarjejeniyar da babu kome a ciki ba. Ya kara da cewa, idan aka yi haka, to, kasar Faransa ba za ta nuna goyon baya ga irin wannan kuduri ba. (Sanusi Chen)