Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-24 21:00:30    
Afrika ta kudu ta bayyana cewa, ba ta fata ta gamu da matsalolin da za su kawo cikas ga shirya wasannin kwallon kafa na cin kwafin duniya

cri
A ranar 23 ga wata, kakakin shugaban kasar Afrika ta kudu Thabo Masebe ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Afrika ba ta fata ta gamu da dukkan ayyukan da za su kawo cikas ga shirya gasar wasannin kwallon kafa na cin kwafin duniya

Tuni dai, wasu kafofin yada labaru suka bayyana cewa, Dalai Lama ya yi shirin halartar bikin "Babban taron zaman lafiya" dangane da wasannin kwallon kafa na cin kwafin duniya na shekarar 2010 da za a yi a birnin Johannesburg a ranar 27 ga wata, amma Afrika ta kudu ta ki amincewa da samar da Visa gare shi. Game da haka, a ranar 23 ga wata, Masebe ya bayyana cewa, yayin da masu shirya taron suka yanke shawarar gayyacin Dalai Lama, ba su yi shawarwari tare da gwamnatin ba. Ya ce, yanzu, hankulan dukkan duniya sun karkata zuwa ga Afrika ta kudu watau mai masaukin baki na wasannin kwallon kafa na cin kwafin duniya na shekarar 2010, Afrika ta kudu ba ta fatan batun Tibet ya janyo hankula daga wajensa.

A sa'i daya kuma, Masebe ya musunta jita-jita cewa, wai gwamnatin Sin ta yi matsin lamba ga Afrika ta kudu, ya ce, Afrika ta kudu ta yanke wannan shawara bisa son ranta, sabo da ta dace da moriyar kasarta.(Bako)