Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-24 16:28:47    
Burin taron koli na kudi na London shi ne daidaita manufar tinkarar matsalar kudi

cri

A ran 23 ga wata, firayim ministan kasar Britaniya Gordon Brown ya bayyana cewa, burin taron koli na kudi na London shi ne shugabannin kasa da kasa su yi shawarwari kan manufar tinkarar matsalar kudi da duk duniya ke fama da ita, da tabarbarewar tattalin arziki, da raguwar yawan cinikayya, kana da matsalar raguwar aikin yi da dai sauransu.

A ran nan, mista Gordon Brown ya yi bayani ga kafofin watsa labaru cewa, da farko, ya kamata a sake tsarin bankuna da na kudi, da kara karfin sa ido kan cinikayya a tsakanin kasa da kasa; Bugu da kari, kamata ya yi a tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki ta kasa da kasa da karuwar yawan cinikayya a mataki mai zuwa; Dadin dadawa, za a ba da taimako ga kasashe mafi talauci da kasashen dake tafiyar da sabbin kasuwanni wajen warware matsalolinsu; Ban da wannan kuma, za a yi gyare-gyare ga hukumomin kudi na duniya kamarsu IMF, da bankin duniya da dai sauransu, don biyan sabbin bukatun kasa da kasa, ciki har da daidaita rabe-raben kasashe masu tasowa a cikin hukumar IMF.

Yayin da yake yin magana kan ra'ayin kariyar yin ciniki, mista Brown ya ce, a gun taron, ya kamata a bullo da tsarin sa ido mai dacewa, da warware batun kariyar yin ciniki don sa kaimi kan kara yawan yin ciniki a kasa da kasa.(Asabe)