Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-24 16:22:12    
Shugaban majalisar wakilan kasar Canada ya gana da tawagar jihar Tibet ta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin

cri

A ran 23 ga wata, shugaban majalisar wakilan kasar Canada Peter Milliken ya gana da tawagar jihar Tibet ta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ke yin ziyara a kasar Canada.

Peter Milliken ya nuna cewa, ziyarar da tawagar ta yi ta bayyana labarai game da bunkasuwar da jihar Tibet ta samu, kuma ya nuna babban yabo ga sakamakon da jihar Tibet ta samu a cikin shekaru 50 da suka wuce.

Shugaban tawagar kuma wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma mataimakin darektan kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet mai ci gashin kanta Shingtsa Tenzinchodrak ya nuna babban yabo ga gudummawa da Peter Milliken ya yi wajen sa kaimi ga dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Canada. Ya nuna cewa, wannan karo ne na farko da tawagar jihar Tibet ta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta kai ziyara a kasar Canada, yana fatan wannan ziyara za ta ba da taimako ga masu mai da hankali a kan jihar Tibet na kasar Canada wajen kara fahimtar halaccin jihar Tibet.

A ran nan da safe, mataimakin ministan ma'aikatar harkokin waje na kasar Canada ya gana da tawagar, kuma ya nuna cewa, gwamnatin kasar Canada tana tsayawa tsayin daka a kan gwamnatin Sin ita kadai ce halatacciyar gwamnati, ba ta nuna goyon baya ga duk ayyukan kawo barakar kasar Sin ba.(Abubakar)