Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-24 16:16:05    
Hu Jintao ya ba da jawabi a gun taron shugabannin kungiyar APEC

cri
Ran 23 ga wata, an gudanar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC na mataki na biyu a karo na 16 ba a hukunce ba a birnin Lima, hedkwatar Peru. Shugaban Sin Hu Jintao ya halarci taron kuma ya ba da jawabi dangane da hadin kan tattalin arziki na yankuna da tsaron dan Adam da sauye-sauyen yanayi da sauransu.

Game da hadin kan tattalin arzikin yankun, shugaba Hu ya nuna cewa, abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne cimma burin taron Bogor cikin lokaci da ciyar da shawarwarin Doha gaba domin samun sakamako tun da wuri. Kasar Sin tana fatan cigaba da ciyar da yunkurin raya tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific gaba tare da bangarori da dama, kuma tana fatan yin nazari game da batun makomar yankin cinikayya mai cin gashin kansa ta Asiya da tekun Pasific.

Game da batun tsaron dan Adam, shugaba Hu ya ce, Sin za ta so ta hada karfi da kungiyar APEC wajen yaki da bala'i.

A fannin sauye-sauyen yanayi, shugaba Hu ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci kan batun dumamar yanayi, kuma ta dauki matakai da yawa domin tinkarar sauyawar yanayi da kyautata muhalli. Bangaren Sin zai cigaba da kokarinsa a nan gaba.(Fatima)