Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-01 17:28:07    
Kasashen Turai da Amurka suna ci gaba da daukar matakai domin tinkarar matsalar kudi

cri
A 'yan kwanakin nan da suka gabata, kasashen Amurka da Rasha da kuma kungiyar tarayyar Turai wato EU sun fitar da sabbin matakai a jere domin tinkarar matsalar kudi ta yanzu.

A ran 30 ga watan jiya, Michael Bloomberg, magajin birnin New York na kasar Amurka ya sanar da wani shiri domin tinkarar matsalar kudi, kuma yana fatan za a iya tallafawa 'yan birnin New York wajen haye wahalolin tattalin arziki ta hanyar inganta zuba jari wajen raya muhimman ayyukan yau da kullum da kuma kara yawan guraban aikin yi da dai sauransu.

Yayin da ake kokari wajen kwantar da kasuwar kadarori ta kasar Rasha, firayim ministan kasar Vladimir Putin ya sanar da wani shiri daban a ran 31 ga watan jiya kan samun goyon baya daga gwamnatin kasar a fannin tattalin arziki, wanda ya kunshe da muhimman abubuwa uku. Kuma shirin zai zama wani tushe wajen daidaita ayyukan da ke tsakanin gwamnatin Rasha da hukumomin da abin ya shafa da kuma bankin tsakiya.

A ran 31 ga watan jiya kuma, kwamitin kula da harkokin kungiyar EU ya amince da manyan shirye-shiryen kasashen Faransa da Holland wajen ceton kasuwanni. Kuma ya zuwa yanzu, kwamitin ya riga ya zartas da shirye-shiryen ceton kasuwanni na membobinsa 7.(Kande Gao)