Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 14:06:08    
Wasu kasashe sun bayyana cewa, za su yi kokari don fuskanci rikicin hada-hadar kudi

cri

A ran 18 ga wata, shugabannin wasu gwamnatocin kasashe da na kungiyoyi sun bayyana cewa, za su kara yin hadin gwiwa don su fuskanci rikicin hada-hadar kudi. Wasu kasashe sun gabatar da sabbin matakai don zaunar da kasuwar hada-hadar kudi.

A ran 18 ga wata, a sansanin David na jihar Maryland, shugaban kasar Amurka Bush ya gana da Nicolas Sarkozy, shugaban kasar Faransa da Jose Manuel Barroso, shugaban kwamitin kungiyar EU, kuma ya sanar da cewa, kasar Amurka za ta yi wani taron koli na duniya kan batun rikicin hada-hadar kudi na duniya. Mr Bush ya ce, tilas ne shugabannin kasa da kasa su yi kokari tare don warware rikicin hada-hadar kudi na duniya.

Ban Ki-moon, babban sakataren MDD wanda ya halarci taron a karo na 12 na shugabannin kasashe masu amfani da Faransanci a birnin Quebec na kasar Canada, ya mika wasika ga Sarkozy, inda ya bayyana cewa, bangaren MDD ya nuna goyon baya ga kungiyar EU da ta ba da shawara kan yin taron koli na hada-hadar kudi na duniya a farkon watan Disamba na shekarar bana.

A ran 18 ga wata, Wu Zuodong, jami'in kula da harkokin kasar kuma shugaban hukumar kula da hada-hadar kudi ta kasar Singapore ya bayyana cewa, gwamnatin Singapore za ta yi kokari don tabbatar da zaunawar kasuwar hada-hadar kudi ta kasar. Idan rikicin hada-hadar kudi na duniya ya haddasa raguwar tattalin arzikin kasar Singapore, gwamnatinta za ta ba da gudummawa ga jama'arta.

A ran 19 ga wata, gwamnatin Koriya ta kudu ta sanar da cewa, za ta ba da kudin samun tabbaci wato garanti da yawansu ya kai dala biliyan 100 don taimakawa bankunan kasar biyan basussuka da kuma sassauta tasirin da rikicin hada-hadar kudi na Amurka ya kawo mata.(Zainab)