Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-16 21:38:04    
An rufe taron koli na kungiyar EU a lokacin kaka

cri

Ran 16 ga wata, a birnin Brussels, an rufe taron shugabanni na kungiyar tarayyar Turai wato EU na lokacin kaka, inda shugabannin kasashe mambobin kungiyar EU suka cimma daidaito kan gudanar da shirin ceton kasuwannin hada-hadar kudi a dukkan kasashe mambobin kungiyar. An tabbatar da wannan shiri a gun taron koli na kasashen da ke amfani da kudin Euro.

A gun taron manema labaru bayan taron kolin, shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa, wadda ke shugabantar kungiyar EU a wannan zagaye ya nuna cewa, shugabannin kasashe mambobin kungiyar EU sun cimma daidaito kan fito da shirin daidaita matsalar kudi na bai daya. Sa'an nan kuma, taron ya tsai da kudurin goyon bayan shirya taron koli domin daidaita rikicin kudi, inda bangarori daban daban za su tattauna kafa sabon tsarin jarin hujja.(Tasallah)