Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 19:03:04    
Rancen kudin da kasar Sin ta samar zai taimakawa kasashen Afirka na dogon lokaci

cri

Ran 10 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Qin Gang kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya ce, rancen kudi na dolar Amurka biliyan 10 da kasar Sin ta samar da su ga kasashen Afirka bisa saukakan sharudda zai taimaka musu wajen warware matsalolin da suke da su yanzu, kuma zai taimaka musu na dogon lokaci wajen kyautata zaman rayuwar jama'a, da kara karfin kansu wajen raya kasa da neman bunkasuwa mai dorewa.

A gun taron ministoci na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da aka yi kwanakin baya, firaminista Wen Jiabao na kasar Sin ya sanar da sabbin matakai 8 da kasar Sin za ta dauka don karfafa hadin gwiwa da Afirka cikin shekaru 3 masu zuwa, ciki har da samar da rancen kudi na dolar Amurka biliyan 10 ga kasashen Afirka bisa saukakan sharudda.

A gun taron manema labaru da aka yi, Mr. Qin Gang ya ce, yanzu kasar Sin ta riga ta tabbatar da wasu muhimman fannonin da za ta ba su rancen kudi, ciki har da manyan gine-gine, aikin gona, ba da ilmi, da kiwon lafiya, da sadarwa, wadannan fannoni suna cin moriyar kasashen Afirka a yanzu da kuma nan gaba. [Musa Guo]