Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 15:22:10    
Kasar Sin ta gabatar da bukatar yin garanbawul kan tsarin tattalin arzikin duniya a fannoni daban-daban

cri
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, a ran 10 ga wata, mataimakiyar shugabar zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin Madam Chen Zhili ta furta a dandalin Beijing na ba da lambar yabo ta Nobel cewa, kasar Sin za ta ba da taimakonta kuma ta kara kaimi ga ayyukan yin garanbawul kan tsarin kudi na duniya, kuma kasar Sin ta ba da shawarar cewa, kamata ya yi, da farko, a kafa tsarin sa ido kan harkokin kudi da kuma tsarin kudi na duniya a duk fannoni.

Madam Chen Zhili ta fadi cewa, kamata ya yi, a tabbatar da ikon yin magana da ikon gani da ido na kasashen masu tasowa a cikin hukumomin kudi na duniya, da kara yawan guraben shugabanni da kasashen dake tasowa suke da su a hukumomin ta yadda za a yi garambawul kan tsarin hukumomin kudi na kasa da kasa. Ban da wannan kuma, kamata ya yi, a kyautata tsarin kungiyoyin kudi da kafa wata hukuma mai amfani wajen tinkarar matsalar kudi da kuma kara karfin gudanarwa na kungiyoyin.(Amina)