Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 10:51:21    
Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da shugabannin kasashen Afrika bakwai

cri
A ran 8 ga wata da safe, a birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da shugabannin kasashen Congo Brazzaville, da Habasha, da kuma Comoros wadanda suka halarci bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da kasashen Afrika.

Yayin da yake ganawa da shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou Nguesso, firaminista Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa tare da kasashen Afrika don tinkarar kalubalen kasa da kasa. Mista Denis Sassou Nguesso ya ce, kasar Congo Brazzaville tana nuna babban yabo ga Sin da ta dukufa kan bunkasa Afrika da yin kokarin tare da Afrika wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya da sauyin yanayi, kuma kasar tana fatan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.

A lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Habasha Meles Zenawi, firaminista Wen Jiabao ya furta cewa, kasar Sin tana iya fahimta da kuma nuna goyon baya ga matsayin kasashen Afrika kan batun sauyin yanayi da bukatunsu, kuma tana fatan kara taimakon juna a tsakaninta da Afrika. Mista Meles Zenawi ya ce, yana fatan kasar Sin za ta kara shiga ayyukan raya tattalin arzikin kasar Habasha, kuma kasar tana son karfafa daidaito da hada kai da Sin a kan batun sauyin yanayi.

Yayin da yake ganawa da shugaban kasar Comoros Ahmed Abdallah Mohamed Sambi, firaminista Wen Jiabao ya ce, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu don kawo zaman alheri ga jama'ar kasar Comoros. Mista Sambi ya bayyana cewa, kasar tana fatan karfafa hadin gwiwa a tsakaninta da Sin don rage talauci da tabbatar da samun bunkasuwa.

A ranar 7 ga wata kuma, mista Wen ya gana da shugabannin kasashen Zimbabwe da Sudan, da Liberiya, da kuma Congo Kinshasa da dai sauransu.(Asabe)