Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 17:49:08    
Wen Jiabao zai halarci bikin bude taron ministoci na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

Ran 27 ga wata, a gun taron manema labaru da aka yi, Mr. Ma Zhaoxu kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin ya sanar da cewa, firaminista Wen Jiabao na kasar Sin zai kai ziyara ga kasar Masar, kuma zai halarci bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Mr. Ma Zhaoxu ya ce, bisa gayyatar da Mahoud Muhammad Nazif firaministan kasar Masar ya yi masa ne, Mr. Wen Jiabao zai kai ziyara ga kasar daga ran 6 zuwa ran 7 ga watan Nuwamba. Mr. Wen Jiabao zai gana da shugaba Mubarak, kuma zai yi shawarwari tare da Nazif. Bangarorin biyu za su yi musa'ayar ra'ayoyi don zurfafa huldar hadin gwiwar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, da sa kaimi ga hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, da harkokin sassa daban daban da ke jawo hankalinsu tare.

Mr. Ma Zhaoxu ya ce, tun daga ran 8 zuwa ran 9 ga watan Nuwamba, za a bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, Mr. Wen Jiabao da wasu shugabannin kasashen Afirka za su halarci bikin bude taron. A yayin wannan taro, za a tattauna yadda aka shimfida ayyukan hadin gwiwa bayan taron koli na Beijing na shekarar 2006, kuma za a shelanta "Sanarwar Sharm el Sheikh" da "Shirin ayyuka na Sharm el Sheikh".