Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-01 14:16:15    
An yi kasaitaccen taron murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin

cri

Ran 1 ga watan Oktoba da karfe 10 na safe, a babban filin Tian'anmen, sassa daban daban na birnin Beijing sun yi babban taron murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi wani muhimmin jawabi, inda ya ce, jama'ar Sin na da karfin zuciya da kuma kwarewa wajen raya kasarsu yadda ya kamata, haka suke a fannin bai wa kasashen duniya gudummawarsu.

A cikin jawabinsa, shugaba Hu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 60 da suka wuce bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, jama'ar Sin sun samu nasarar daidaita kalubaloli da wahalhalu da kuma barazana masu nau'o'i daban daban, sun samu manyan nasarorin da ke jawo hankalin kasashen duniya sosai. Nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje, da sa kaimi kan bunkasuwar kimiyya da fasaha, da samun jituwa a zaman al'ummar kasar, da raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni. Sa'an nan kuma, kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar "dinkuwar kasar cikin lumana" da ta "kasa daya amma tsarin mulkin 2", za ta yi kokarin tabbatar da samun dauwanammiyar wadatuwa da kwanciyar hankali a yankunan musamman na Hong Kong da Macao, da sa kaimi kan raya hulda a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, za ta ci gaba da yin gwagwarmaya domin dinkuwar kasar Sin gaba daya.

Dadin dadawa kuma, shugaban Hu ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar 'yancin kai ba tare da tsangwama ba kuma cikin ruwan sanyi a harkokin diplomasiyya, za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, tare kuma da bin manyan tsare-tsaren bude kofa ga waje domin neman moriyar juna da samun nasara tare. Ban da wannan kuma, bisa manyan ka'idoji 5 na yin zaman tare cikin lumana, Sin za ta bunkasa hadin gwiwar abokantaka da dukkan kasashen duniya, za ta sa kaimi kan raya duniya mai jituwa da dauwamammen zaman lafiya da wadatuwa tare.

A yayin bikin duba faretin soja da aka yi bayan jawabin shugaban Hu,rukunnoni 56 na rundunar sojan kasar Sin sun nuna sabon sakamakon da Sin ta samu a fannin aikin soja.

Bayan bikin duba faretin soja, fararen hula daga sassa daban daban dubu 100 da motoci 60 masu launuka daban daban sun yi kasaitaccen maci cikin fara'a a filin Tian'anmen.(Tasallah)