Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 21:52:22    
Hu Jintao da sauran manyan jami'an gwamnatin Sin sun gana da wakilan kwararrun da daliban da suka gama karatu a kasashen waje

cri

A ran 30 ga wata a nan birnin Beijing, Hu Jintao da Wen Jiabao da kuma Xi Jinping da sauran manyan jami'an jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar sun gana da wakilan kwararrun dake kasashen waje da kuma daliban da suka kammala karatu a kasashen waje wadanda za su halarci bikin duba faretin soja bisa gayyata.

Hu Jintao ya yi jawabin cewa, sabuwar kasar Sin ta samu kyakkyawan sakamako bayan da ta kafu a cikin shekaru 60 da suka gabata, amma duk an sheda cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa, za ta ci gaba da zama a cikin matakin farko na zaman gurguzu, tana bukatar kokarin da dukkan Sinawa ciki har da kwararru da daliban dake kasashen waje suka yi don tabbatar da zaman gurguzu na zamani.

Hu Jintao ya ce, ya yi fatan Sinawa kwararrun dake kasashen waje za su ci gaba da ba da gudummawa ga kasarsu ta haihuwa don samun bunkasuwar al'ummar Sin. Kana yana fatan daliban da suka gama karatu a kasashen waje za su yi kokarin aiki a gida don kara samun sakamako mai kyau.(Lami)