Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 19:02:14    
Gwamnatin kasar Sin ta shirya gagarumar liyafa domin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin

cri

A ran 30 ga wata da maraice, majalisar gudanarwa ta kasar Sin, wato gwamnatin kasar ta shirya gagarumar liyafa a nan birnin Beijing domin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. Muhimman jami'ai da baki fiye da dubu 4 na kasar Sin da na kasashen waje sun halarci wannan liyafa domin taya murna a yayin wannan biki tare.

A yayin liyafa, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya yi wani jawabi cikin fara'a, inda ya ce, da kasar Sin ta samu kyakkyawan sakamako ne cikin shekaru 60 da suka gabata bisa kokarin da jama'ar duk kasar da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suka yi bayan da suka aiwatar da tunanin gurguzu da ke dacewa da halin musamman na kasar.

Mr. Wen ya bayyana cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufofin tafiyar da harkoki da kansu a yankunan da aka fi samun kananan kabilu da manufofin kabilu da na addinai kamar yadda take yi yanzu, kuma za ta karfafa da kuma raya huldar zaman daidaiwa daida da gama kai da taimakawa juna da zumunci bisa tunanin gurguzu a tsakanin kabilu daban daban. A waje daya, Wen Jiabao ya jaddada cewa, za a ci gaba da bin manufar "aiwatar da tsare-tsaren zaman al'umma iri biyu a cikin kasa daya" domin tabbatar da kwanciyar hankali da bunkasuwa a yankunan musamman na Hongkong da Macau cikin dogon lokaci. Bugu da kari, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan matsayinta na kasancewa daya tak a duniya, kuma za ta hada kan 'yan uwa na Taiwan domin kafa wani sabon halin da ake ciki a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan a fannin raya hulda a tsakaninsu cikin lumana, kuma za ta yi kokarin samun hadin kan kasar Sin cikin lumana.

Da misalin karfe 10 na safe ran 1 ga watan Oktoba, agogon Beijing, za a shirya gagarumin bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a filin Tian'anmen na birnin Beijing. A yayin bikin, shugaba Hu Jintao zai bayar da wani muhimmin jawabi, kuma za a yi bikin faretin sojoji, jama'ar birnin Beijing za su kuma yi maci cikin fara'a. (Sanusi Chen)