Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 10:39:07    
Za a gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin a gobe

cri
A ranar Alhamis, daya ga watan Oktoba, a filin Tian Anmen na birnin Beijing, za a gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin. Tun da ran 29 ga wata da dare, hukumomin da za su halarci gagarumin bikin sun riga sun shiga filin Tian Anmen daya bayan daya don share fage a gabannin gudanar da gagarumin bikin da kuma nishadin dare mai kayatarwa. 

A misalin karfe 10 na safiyar wannan rana, a filin Tian Anmen, kungiyoyi daban daban na babban birnin kasar za su gudanar da babban taron murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, kuma shugaban kasar Mr. Hu Jintao zai yi jawabi. Daga baya, za a yi bikin faretin soja da na fararar hula.

A ran nan da dare, mutane fiye da dubu hamsin za su yi nishadi mai kayatarwa a filin, inda za a kuma yi wasan wuta na tsawon mintoci 30.

Ban da wannan kuma, a ran nan, gidan radiyon kasar Sin zai watsa shirye-shiryen bukukuwa kai tsaye ta hanyoyi biyar wato watsa shirye-shirye dangane da bukukuwa ga kasashen ketare da gida, da kuma watsa shirye-shirye ta hanyar bidiyo da hotuna na Internet da dai sauransu, ta yadda za a watsa shirye-shiryen bukukuwa kai tsaye daga dukkan fannoni.(Asabe)