Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 10:34:15    
An shirya liyafa don taya murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin

cri

A ran 29 ga wata da dare, ofishin gudanarwa na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da sashen kula da harkokin dunkulallun jam'iyyun siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, da ofishin kula da harkokin 'yan kasar Sin dake a ketare da ofishin kula da harkokin 'yan Hongkong da na Macau da kuma ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin sun shirya wata liyafa don taya murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin. Zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Jia Qinglin, da zaunannen memban ofishin siyasa na kwamtin tsakiya na jam'iyyar kuma mataimakin shugaban kasar Xi Jinping, da zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kuma mataimakin firayin ministan kasar Li Keqiang da kuma abokai fiye da dubu 4 na gida da na waje sun taru waje daya don taya murnar cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin.

Mr Jia Qinglin ya yi wani jawabi a gun liyafar cewa, a cikin shekaru 60 da suka wuce, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta jagoranci jama'a 'yan kabilu daban daban na duk kasa ga samun manyan nasarori. Gwamnatin tsakiya za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar "kasa daya tak amma da tsari iri biyu" da muhimmiyar doka, da nuna goyon baya ga gwamnonin yankin Hongkong da na Macau da gwamnatocinsu wajen gudanar da ayyukansu bisa doka, da kara yin hadin gwiwa tare da babban yankin kasar, da yin kokari wajen bunkasa tattalin arziki da kyautata rayuwar jama'a da inganta tafarkin demokuradiyya da samun jituwa don kirkiro kyakkyawar makoma ta yankunan biyu.

Mr Jia Qinglin ya jaddada cewa, a cikin shekaru 60 da suka wuce, jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin Sin sun yi namijin kokari wajen warware batun Taiwan. Tun watan Mayu na bara, an samu babban sauyi kan dangantakar dake tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, an kuma bullo da sabon hali na yin mu'amala tsakaninsu a dukkan fannoni, lallai akwai kyakkyawar makoma ta inganta dangantakar dake tsakanin gabobi biyu cikin lumana.(Zainab)