Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-25 21:14:55    
An shirya taron liyafa don taya murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiya tsakanin Sin da Rasha

cri
A ranar 25 ga wata da yamma, an shirya taron liyafa a zauren babban dakin taron jama'a na kasar Sin, don taya murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasashen Sin da Rasha, da kafa majalisar sada zumunta tsakanin kasashen biyu. Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya halarci taron, da kuma yin jawabi.

A cikin jawabinsa, Mr. Jia Qinglin ya bayyana cewa, ya kamata bangarorin biyu su kiyaye dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare, don inganta bunkasuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Kazalika kuma, kamata ya yi a ci gaba da yin mu'ammala tsakanin manyan shugabanni, da jami'ai bisa mataki daban daban na kasashen biyu, da kula da babbar moriyar juna, da sa himma don gudanar da hakikanin hadin kai a fannoni daban daban, da kuma kokarta yin cudanya ta sada zumunta tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Kafin taron liyafar kuma, Mr. Jia Qinglin ya gana da shugaban majalisar sada zumunta tsakanin Rasha da Sin Mikhail Titarenko. (Bilkisu)