Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-12 15:29:18    
(Sabunta)An gudanar da bikin tunawa da cika shekara 1 da aukuwar babbar girgizar kasa ta yankin Wenchuan

cri

A ran 12 ga wata da yamma, an gudanar da bikin tunawa da cika shekara 1 da aukuwar babbar girgizar kasa a yankin Wenchuan na lardin Sichuan a birnin Yingxiu, wanda shi ne cibiyar girgizar kasar. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin da wakilan bangarori daban daban fiye da dari 1 sun halarci bikin.

Da karfe 2 da minti 28 na yamma, dukkan masu halartar bikin sun tashi sun nuna juyayi ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da jaruman da suka mutu yayin da suke yin ayyukan ba da agaji a girgizar kasar.

Tare da taken kasar Sin mai karfi, tutar kasar ta tashi.

Hu Jintao ya yi wani jawabi. Bayan da ya yi jawabin, Hu Jintao ya zo gaban ganuwar tunawa da girgizar kasar, ya ajiye wani fure mai ruwan zinari. Li Keqiang da sauran shugabannin kasar bi da bi ne sun ajiye furanni a gaban ganuwar.

Kuma wakilan bangarori daban daban masu halarci bikin sun ajiye fure a gaban ganuwar.

A ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008, girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 8 bisa ma'aunin Richter ta faru a yankin Wenchuan na lardin Sichuan, wadda ya haddasa mutuwar mutane da yawa da jikkata jama'a masu dimbin yawa da kuma manyan hasarori. A cikin shekara daya da ta wuce, an gudanar da ayyukan sake ginawa yadda ya kamata bayan aukuwar girgizar kasar, kuma jama'ar yankunan da bala'in ya shafa suna zama yadda ya kamata.(Zainab)