Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-04 21:38:15    
Yawan kudaden da gwamnatin kasar Sin ta zuba wajen farfado da yankunan da girgizar kasa ta shafa ya kai kusan yuan biliyan 85 a bana

cri
Bisa abarin da wakilinmu ya samo daga ma'aikatar kudi ta kasar Sin a ran 4 ga wata, an ce, kawo yanzu, gaba daya yawan kudaden da gwamnatin kasar Sin ta zuba a wannan shekara don farfado da yankunan da girgizar kasa ta shafa ya kai kusan kudin Sin yuan biliyan 85, wanda ya kai kashi 65% na kasafin kudi na shekarar.

Kididdigar da ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta yi ta nuna cewa, kasafin kudi na kusan yuan biliyan 85 na farfado da yankunan da girgizar kasa ta shafa ya samar da tabbaci mai karfi na farfado da lardunan Sichuan da Gansu da Shanxi da girgizar kasa ta galabaitar, musamman ma ta fannin farfado da gidajen noma da makarantu da asibitoci da dai sauran manyan ayyuka.

Ban da wannan, a ran 4 ga wata, babban sakataren kungiyar Red Cross ta kasar Sin, Mr.Wang Rupeng ya bayyana a birnin Beijing cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, kungiyar ta riga ta karbi kudade da kayayyaki taimako da aka bayar da yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan 392.(Lubabatu)