Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-28 18:20:40    
An yi taron murnar ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet

cri

A ran 28 ga wata da safe, a filin da ke gaban fadar Potala a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet ta kasar Sin, an yi taron murnar ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet, kuma wakilai sama da dubu 13 da suka zo daga bangarori daban daban na Tibet sun halarci taron.

Shugaban hukumar jihar Tibet mai cin gashin kanta, Qiangba Puncog ya shugabanci taron, kuma wakilan bangarori daban daban sun yi jawabi daya bayan daya.

Tsondre, wani mazaunin birnin Lhasa dan shekaru 69, wanda ya taba kasancewa bawa manomi a tsohuwar Tibet, ya yi jawabin cewa, tsai da ran 28 ga watan Maris na kowace shekara da ya zama ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma buri ne na miliyoyin bayi manoma da suka sami 'yancinsu, kuma muna nuna cikakken goyon baya gare shi.

Zhang Qingli, sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin a jihar Tibet, ya yi jawabin cewa, a cikin shekaru 50 da suka gabata, cigaban Tibet ta fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu ya burge duniya kwarai da gaske. Ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da daukaka cigaban tattalin arzikin Tibet da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a, haka kuma za ta yi kokarin kiyaye tsaron kasar da kwanciyar hankali a Tibet. (Lubabatu)