Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 21:51:31    
Shugaban majalisar CPPCC ya gana da wakilan Sin da na kasashen waje da za su halarci taron dandalin tattaunawar addinin Buddah na duniya

cri

A ran 27 ga wata a birnin Wuxi na kasar Sin, shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin, Mr.Jia Qinglin ya gana da wakilan Sin da na kasashen waje da za su halarci taron dandalin tattaunawar addinin Buddah na duniya.

A yayin da yake ganawa da wakilan bangaren addinin Buddah da suka zo daga babban yankin kasar Sin da yankunan Hongkong da Macao da kuma Taiwan na kasar, Jia Qinglin ya yi fatan cewa, bangaren addinin Buddah na yankunan nan hudu za su hada kan mabiya addinin, kuma su kara gudanar da ayyuka na sanyaya ran jama'a da daidaita sabaninsu.

A yayin da yake ganawa da wakilan bangarorin addinin Buddah na kasashen ketare, Mr.Jia Qinglin ya yi nuni da cewa, Sin kasa ce da ke da mabiya addinai da dama, kuma tana bin manufar baiwa jama'a 'yancin bin addinan da suka ga dama, wanda kuma ya shaida kiyaye moriyar jama'a da hakkin dan Adam da Sin ke yi. Gwamnatin kasar Sin na baiwa bangarorin addinai na kasar da su inganta mu'amala tare da takwarorinsu na kasashen ketare bisa tushen samun 'yancin kai da zaman daidaito da kuma girmama juna.

Za a bude taron dandalin tattaunawar addinin Buddah na duniya karo na biyu ne a ran 28 ga wata a birnin Wuxi na kasar Sin.(Lubabatu)