Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-26 21:19:35    
Ba za a iya kawar da bayyanar aikata laifuffuka da kungiyar Dalai Lama ta yi ba, a cewar kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin

cri
A gun taron manema labaru da aka shirya a ranar 26 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'arkatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya ce, lamarin aikata laifuffukan doke-doke, da barnata kayayyaki, da kwashe kayayyakin jama'a, da cinnawa wurare wuta da suka auku a ranar 14 ga watan Maris na shekarar da ta wuce, aikin tada hankalin jama'a ne da kungiyar Dalai Lama ta shirya, kuma nakirci ne da ta kulla tare da 'yan a-ware na Tibet da ke ketare. Hakikanin abu ya shaida laifuffukan da kungiyar Dalai Lama ta yi, ba za a iya kawar da bayyanar wadannan laifufuka da ta yi ba.

A lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da faifan bidiyo na lamarin da ya auku a ranar 14 ga watan Maris da kungiyar Dalai Lama ta bayar, Mr. Qin Gang ya ce, a bayyane ana iya ganin abubuwa da ba na gaskiya ba ne a cikin wannan faifan bidiyo. Wannan ne kuma hanyar da kungiyar Dalai Lama ke bi ko da yaushe. Mr. Qin Gang ya kara bayyana cewa, a da kungiyar Dalai Lama ba ta samu sa'ar tabbatar da makarkashiyarta ba, kuma ba za ta cimma burinsu na neman kawo baraka ga Sin, da kawo tashe-tashen hankula a Tibet ba. (Bilkisu)