Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-25 21:20:22    
'Yan diplomasiyya na Afrika da ke kasar Sin sun yaba wa katafaren bikin tunawa da zagayowar shekaru 50 da aka yi gyare-gyaren demokuradiyya a jihar Tibet

cri

A ranar 25 ga wata da yamma, bisa goron gayyata da ma'aikatar harkokin waje ta Sin ta yi, aminan kasashen waje da yawansu ya wuce 150 ciki har da 'yan diplomasiyya da wakilan kungiyoyin duniya fiye da 60 sun halarci katafaren bikin tunawa da zagayowar shekaru 50 da yin gyare-gyaren demokuradiyya a jihar Tibet a babban dakin al'adu na kananan kabilu na kasar Sin, kuma sun yi mu'amala da kwararru a fannin Tibet a wurin.

Bayan da suka kammala ziyara, 'yan diplomasiyya sun bayyana cewa, wannan biki ya nuna mana bunkasuwar da jihar Tibet ta samu, kana kuma sun kara ilminsu wajen ainihin abin da ya auku a jihar Tibet, da makarkashiya da rukunin Dalai Lama ya kulla.

Mukadashin jakadan ofishin jakadancin Ghana da ke kasar Sin Akwasi Agyeman Agyare ya bayyana cewa, idan ana son sanin ainihin abin da ya auku a jihar Tibet, sai wanda ya zo ya gani. Da ma, ta hanyar fina-finai, mu kara samun ilmi a kan batun Tibet, amma dan kadan ne, bayan mun gama biki na yau, mun kara sanin ainihin abin da ya auku a can. Rukunin Dalai su kan yada jita-jita a kan harkokin Tibet, a ganina, sabo da tsoron asirin ya tonu."

Jakadan Somaliya da ke kasar Sin H.E. Mr. Mohamed Ahmed Awil ya bayyana cewa bikin tunawa da zagayowar shekaru 50 da yin gyare-gyaren demokuradiyya a jihar Tibet biki na mai muhimmanci sosai, masu shirya bikin sun zage damtse sosai wajen shirya wannan biki, ko wane daki na da hotuna na tarihi masu tarin yawa, dukkansu sun kawo sauki, da mu kara samun ilmi a kan bunkasuwar Tibet cikin shekaru 50 da suka gabata. A ganina, wadanan hotuna kamar shaidu ne, za su iya nunawa mutane ainihin abin da ya auku. Yanzu ina so in gaya wa dukkan masu yin suka da cewa, ga shaidu suna nan, wannan shi ne abin da na gani.(Bako)