Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-24 20:42:10    
Sin na kin yarda da kowace kasa da ta samar wa Dalai Lama saukin gudanar da ayyukan neman ballewar Tibet

cri

A gun taron manema labarai da aka kira a ran 24 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Qin Gang ya bayyana cewa, Sin na tsayawa tsayin daka wajen kin yarda da kowace kasa da ta samar wa Dalai Lama saukin gudanar da ayyukan neman ballewar Tibet.

A yayin da yake amsa tambayar manema labarai game da kin bai wa Dalai Lama izinin shiga Afirka ta kudu da gwamnatin kasar ta yi, Mr.Qin Gang ya ce, dukan kasashen duniya, illa dai suna girmama mulkin kai na Sin da cikakkun yankunanta, da kuma nacewa ga bin manufar Sin daya tak a duniya da kuma kin yarda da 'yancin kan Tibet, to, Sin na nuna musu yabo. Qin Gang ya kara da cewa, Dalai Lama ba wai wani mabiyin addini na gaskiya ba, a'a, hasali ma shi dan siyasa da ke neman jawo baraka ga kasarsa ta mahaifa da kuma lalata hadin kan al'ummar kasar, kuma yanzu karin kasashe da jama'arsu sun fara gano ainihin halinsa. Sin na tsayawa tsayin daka kan kin yarda da gwamnatin kowace kasa da ta tuntubi Dalai Lama ko kuma samar masa sauki ko dandali wajen gudanar da ayyukan jawo baraka ga kasar Sin, haka kuma tana kin yarda da kowace kasa da ta yi amfani da batun Tibet wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin.

A ran 22 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta Afirka ta kudu ta sanar da cewa, gwamnatin kasar ba ta ba wa Dalai Lama goron gayyatar zuwa taron zaman lafiya ba, wanda za a yi a ran 27 ga wata a birnin Johannesburg, kuma a cewar ma'aikatar, kudurin ya dace da babbar moriyar kasar.(Lubabatu)