Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-23 22:24:19    
Ngapoi Ngawang Jigme yana fatan Dalai Lama zai fid da matsayinsa na neman 'yancin kan Tibet'

cri
A ranar 24 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin za ta bayar da bayanin da Ngapoi Ngawang Jigme, wato mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin a karo na 11 ya yi, inda Ngapoi Ngawang Jigme ya ce, yana fatan Dalai Lama zai yi watsi da ra'ayinsa na neman "'Yancin kan Tibet", da kuma sake komowa matsayin kaunar kasa.

A cikin bayanin, Ngapoi Ngawang Jigme ya ce, a matsayinsa na wani mutum da ya taba zama a tsohuwar Tibet, da sabuwar Tibet, yana ganin cewa, ta nacewa ga bin hanyar gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar kawai, jama'ar Tibet za su iya gudanar da harkoki da kansu, kuma Tibet za ta iya samun cigaba, jama'a za su iya zaman alheri.

Bayan haka kuma, Ngapoi Ngawang Jigme ya ce, tarihi ya shaida cewa, tabbas ne aikin neman "'yancin kan Tibet" zai ci hasara.