Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-22 19:37:33    
Panchen na 11 Erdeni Qoigyi Gyibo ya yi bayani don tunawa da cikon shekaru 50 da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet

cri
Jaridar People's Daily da aka buga a ranar 23 ga wata, ta bayar da bayanin da Panchen na 11 Erdeni Qoigyi Gyibo ya yi don tunawa da cikon shekaru 50 da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet. A cikin bayanin ya ce, an samu ci gaban tsarin al'ummar Tibet irin na tarihi ta hanyar yin gyare-gyaren dimokuradiya a Tibet. Hakikanin abu ya nuna cewa, sai dai jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ne kawai ke iya bai wa bayi manoma mutunci da 'yancin kai.

Bayan haka kuma, bayanin ya ce, tun shekaru 50 da suka wuce da aka yin gyare-gyaren dimokuradiya a Tibet, jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta tana gudanar da sha'anoni daban daban na jihar ita da kanta, kuma tana tabbatar da 'yancin kan jama'ar Tibet a fannonin gaji da bunkasa al'adun gargajiya, da kuma amince da addininsu. Lallai a cikin yunkurin zamanintar da gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin, sabuwar jihar Tibet na samun cigaba da sauri, kuma ta samu nasarorin da ke jawo hankalin duniya.

Panchen na 11 Erdeni Qoigyi Gyibo ya bayyana cewa, zai ci gaba da gado da raya kyakkyawar al'adar tsoffafin Panchan irin ta kaunar kasa da addininsu, da kuma kiyaye kasa, da kawo moriya ga jama'a. (Bilkisu)