Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-22 17:42:19    
Gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokari don rage illar da rikicin hada-hadar kudi ke kawowa kasar

cri
Ranar 22 ga wata, a nan birnin Beijing, a yayin da yake halartar taron shekara-shekara na dandalin tofa albarkacin baki tsakanin manyan jami'ai a kan harkokin neman bunkasuwa na shekara ta 2009, mataimakin ministan kudi na kasar Sin Mista Wang Jun ya bayyana cewa, akwai abubuwan rashin sanin tabbas, da wahaloli, da kalubaloli da dama a cikin makomar tattalin arzikin kasar, amma gwamnatin kasar Sin za ta yi namijin kokari domin rage illar da rikicin hada-hadar kudi ke kawowa kasar.

Wang Jun ya ce, a halin da ake ciki yanzu, gwamnatin kasar Sin tana gaggauta aiwatar da jerin manufofi don raya tattalin arzikin kasar, haka kuma an riga an samu sakamakon mai kyau a wasu yankuna da sana'o'i a kasar. Ana da imanin cewa, bisa sakamakon kokarin da ake yi, yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 8 bisa dari a wannan shekara.

Wang Jun yana fatan gwamnatocin kasashe daban-daban, da kungiyoyin kasa da kasa, gami da kamfanoni dabam-dabam za su zama tsintsiya madaurinki daya don shawo kan rikicin hada-hadar kudi.

Har wa yau kuma, a wannan rana, mataimakin shugaban bankin duniya mai kula da harkokin yankunan gabashin Asiya da tekun Pacific Mista James W. Adams ya ce, ya zuwa yanzu, matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka a fannin manufofin hada-hadar kudi don tinkarar rikicin kudi, suna dacewa da hakikanin halin da ake ciki.(Murtala)