Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 17:08:56    
Sin na kokarin kare darajar kudinta bisa matsayin nuna daidaito da na gaskiya

cri
A ran 13 ga wata, firayim ministan Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, burin Sin shi ne kare darajar kudinta bisa matsayin nuna daidaito da na gaskiya. Sin ita da kanta ta tsai da darajar kudinta, babu tawa kasa da za ta iya kawo matsin lamba ga karuwa ko raguwar darajar kudin Sin.

A ran nan a nan Beijing, an rufe taron majalisar wakilan jama'ar Sin. Yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru a gun taron watsa labaru da aka yi bayan taron, mista Wen Jiabao ya ce, tun da aka yi gyare-gyaren darajar musanyar kudi a watan Yuli na shekarar 2005, darajar kudin Sin ta karu da kashi 21% kan darajar dala. Musamman ma a bana, sabo da raguwar darajar kudaden kasashen Turai da na Asiya, darajar kudin Sin tana karuwa. Hakan ya kawo matsin lamba ga Sin wajen yin fiton kayayyaki. Sabo da haka, cewar darajar kudin Sin ta ragu ba ta dace da hakikanin halin da ake ciki ba.(Asabe)