Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-12 10:16:52    
An rufe taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin na shekarar bana 

cri

A ranar 12 ga watan Maris da safe, a nan birnin Beijing, an rufe taro na biyu na kwamitin 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, inda aka samu halartar shugabannin kasar Sin kamarsu Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao, da Jia Qinlin, da dai sauransu.



Jia Qinlin, shugaban majalisar kuma dan zaunannen kwamiti na hukumar siyasa ta tsakiya ta Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya shugabanci bikin rufe taron, inda ya yi jawabin cewa, 'yan majalisar sun tattauna kan yadda za a kiyaye bunkasuwar tattalin arziki mai karko da kuma sauri, da kare zaman jituwa da kwaciyar hankali a cikin zaman al'umma, ta yadda suka ba da shawarwari masu muhimmanci ga gwamnatin kasar Sin. A gaba daya, 'yan majalisar sun samar da jawabai 769, da shirye-shirye 5571, da rahotanni kan ra'ayin jama'a fiye da 900, da dai sauransu.

Mista Jia ya ce, wannan shekara tana da muhimmanci sosai, domin ana neman samun sabon cigaba duk da cewa ana fuskantar kalubale a gida da kuma waje, shi ya sa ya bukaci majalisar da ta ci gaba da samar da gudumawa don neman cika burin kasar na raya tattalin arziki da al'umma.(Bello Wang)