Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 20:31:31    
Ya kamata rundunar sojin kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan kiyaye mulkin kan kasar da cikakken yankinta

cri

Ranar 11 ga wata, babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin soja na tsakiya Mista Hu Jintao ya jaddada cewa, kamata ya yi a yi kokarin bunkasa harkokin tsaron kasar, da zamanintar da rundunar sojin kasar, da tsayawa tsayin daka kan kiyaye mulkin kan kasa, da cikakken yankin kasa, gami da tabbatar da yanayin tsaro a kasar, ta yadda za'a bada cikakken tabbaci ga kare babbar moriyar kasa, da tabbatar da kwanciyar hankali a kasar.

Hu Jintao ya nuna cewa, ya kamata a nace ga zamanintar da rundunar sojin kasar Sin, musamman ma a maida hankali kan inganta kwarewar sojoji, da horas da su a fannin aikin soja. A waje guda kuma, kamata ya yi a nuna hazaka wajen yin gyare-gyare ga harkokin tsaron kasar da rundunar sojin kasar, don sanya kuzari da bada tabbaci ga raya harkokin tsaro na kasar da inganta kwarewar rundunar sojin kasar ta hanyar kimiyya.(Murtala)