Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 14:45:33    
Tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin babban tsari ne na siyasa kuma tamkar muhimmin jigo ne na demokuradiyya

cri
Jaridar People's Daily ta rubuta wani sharhi a ran 11 ga wata, inda ta ce, tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin babban tsari ne na siyasa kuma tamkar muhimmin jigo ne na demokuradiyya.

Sharhin ya ce, tsarin majalisar wakilan jama'a yana da muhimmanci game da bunkasuwar siyasa ta irin mulkin gurguzu mai alamar musamman ta Sin, ba ma kawai ya bayyana moriya da fatan duk jama'ar Sin ba ne, hatta ma ya zama muhimmin tsarin siyasa da wayewar kai na irin mulkin gurguzu.

A matsayin wani irin tsarin mulkin kasa, majalisar wakilan jama'ar Sin ta bayyana demokuradiyya irin ta mulkin gurguzu, kuma shi ne muhimmiyar hanyar samun ikon gudanar da harkokin jama'a, da ya tabbatar da moriyar jama'a.

A cikin shekaru 50 da suka wuce, tsarin majalisar wakilan jama'ar Sin ya tabbatar da ikon jama'a na gudanar da harkokin kasa da ba da tabbaci ga hukumomin gwamnatin kasar don aiwatar da ayyuka bisa daidaici tare da samun sakamako, da kiyaye dinkuwar duk kasa da hadin kan kabilu daban daban.

Tsarin majalisar wakilan jama'ar Sin ya dace da halin da ake ciki a kasar Sin, kuma ya bayyana ainihin mulkin gurguzu na kasar Sin, wanda shi ne muhimmin tsarin siyasa da ya tabbatar da ikon jama'ar na gudanar da harkokin kasar Sin.(Zainab)