Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 14:07:29    
Mutanen kasashen waje a Sin sun darajanta kyakkyawar mokomar tattalin arziki ta Sin

cri

Mutanen kasashen waje a Sin sun mai da hankula sosai kan taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa da na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, yayin da suke zantawa da manema labaru, sun bayyana cewa, makomar Sin tana cikin hali mai kyau, kasashen duniya suna sanya ran muhimmiyar rawar da Sin za ta taka.

Manema labaru na jaridar "Rodong Sinmun" ta hukumomin tsakiyar jam'iyyar Rodong ta kasar Koriya ta arewa dake birnin Beijing sun bayyana cewa, Sin tana da kyakkyawar makoma. Shekarar bana shekara ce ta "Sada zumunta tsakanin Koriya ta arewa da Sin", jaridar Rodong Sinmun tana gabatar da sakamakon da Sin ta samu da zumunta tsakanin jama'ar kasashen biyu cikin yakini. Manema labaru na kamfanin dillancin labaru na VNA a birnin Beijing sun furta cewa, tattaunawa kan kauyuka da aikin gona da manoma da aka yi a gun taron majalisun biyu ta fi jawo hankulan kafofin watsa labaru na Vietnam, matakan da Sin ta dauka na bunkasa aikin noma suna da ma'ana sosai ga Vietnam.

Shugaban hukumar kula da harkokin Sin da Mongoliya ta bankin duniya Du Dawei ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta dauki kwararran matakai na kara wa tattalin arziki kaimi ta hanyar kara zuba jari kan manyan ayyukan zaman yau da kullum da kara kebe kudi ga sha'anin tarbiyya da na kiwon lafiya da na ba da tabbaci ga zaman alumma da sauransu. Ya nuna imanin cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin cikin sauri mai dorewa za ta ba da gudummawa wajen tinkarar koma bayan tattalin arzikin duniya.(Fatima)