Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 20:20:51    
Yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet ta kasar Sin abu ne mai babbar ma'ana a harkokin 'yantar da bayi a duniya

cri
Ranar 10 ga wata, a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, abu ne mai muhimmiyar ma'ana a cikin harkokin 'yantar da bayi a dukkan duniya, wanda kuma shi ne babban cigaba da aka samu a fannin raya hakkin bil'adama na duniya, da babbar gudummawar da jama'ar kasar Sin, ciki har da 'yan kabilar Tibet suka bayar ga tsarin dimokuradiyya da sha'anin hakkin dan Adam na duniya.

Ma Zhaoxu ya yi wannan furuci ne a yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida dangane da batutuwan dake shafar Tibet a wajen taron manema labaru da aka shirya a wannan rana. Ya ce, tun shekara ta 1959, aka soma gudanar da gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a Tibet, inda aka 'yantar da miliyoyin bayi manoma, da ba su cikakken 'yancin kai. A cikin shekaru sama da 50 da suka gabata, jihar Tibet ta samu manyan sauye-sauye a fannoni da dama, ciki har da siyasa, da tattalin arziki, da kuma al'adu.(Murtala)