Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 16:48:34    
Masana'antun kasar Sin suna samun kyawawan alamu

cri

A ran 10 ga wata, a birnin Beijing, ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin Li Yizhong ya nuna cewa, yanzu masana'antun kasar Sin suna samun kyawawan alamu, amma suna cikin lokaci mafi tsanani, duk da haka ba wanda zai iya cewa halin da masana'antun kasar Sin suke ciki ya canza.

A gun taron manema labaru da aka shirya a ran nan a taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na shekara-shekara da aka saba yi, Li Yizhong ya nuna cewa, yanzu, yawan wutar lantarki da masana'antun kasar Sin suke yin amfani da ita ya ragu, kuma ana maido da masana'antun karafa ta kasar Sin, yawan karafa da aka samu a cikin watanni 2 da suka wuce ya karu da kashi 3.1 cikin kashi dari bisa makamancin lokaci na bara, kuma yawan siminti da aka samu ya karu da kashi 17 cikin kashi dari, yawan motocin da aka kera ya kai matsayin na watan Yulin bara. Wadannan duk kyawawan alamu ne da masana'antun kasar Sin suka samun.

A sa'i daya, Li Yizhong ya nuna cewa, masana'antun kasar Sin suna cikin lokaci mafi tsanani, ba wanda zai iya cewa halin da masana'antun kasar Sin suke ciki ya canza.(Abubakar)