Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 16:43:15    
Gwamnatin Sin tana bincike kan yadda kamfannonin Sin za su samu ci gaba a fannin sayen kamfanoni a kasashen ketare

cri
A gun taron manema labaru na taron majalisar wakilan jama'ar Sin na shekara shekara da aka saba yi a ran 10 ga wata a birnin Beijing, ministan kasuwanci na kasar Sin Chen Deming ya bayyana cewa, gwamnatin Sin tana bincike kan yadda manyan kamfannonin Sin za su samu ci gaba a fannin ba da taimako ga kasashen ketare da yin ayyuka a kasashen waje da kuma sayen kamfanoni da dai sauransu.

Mista Chen Deming ya ce, yayin da kungiyar sayen kayayyaki ta Sin da ya jagoranta ke bakunci a kasashe hudu dake yammacin Turai a kwanakin baya, kasashe da yawa sun gabatar da kamfannoni da yawa ga Sin da ke fatan hadin kai da Sin, ciki har da wasu kamfannonin samar da tufafi. A gami da wannan, gwamnatin Sin tana daukar ra'ayi mai yakini, kuma tana fatan da mara wa manyan kamfannonin Sin baya da su samu ci gaba a kasashen waje.

Ban da wannan kuma, Chen Deming ya nuna cewa, wasu kasashen suna ganin cewa, kasar Sin ta mai da hankali kan samun rarar kudi wajen yin cinikayya tsakanin kasa da kasa kawai. An yi wannan irin bayani ba bisa adalci ba kuma ba bisa gaskiya ba. Kasar Sin ta samu rarar kudi wajen yin cinikayya, amma tana kokarin daidaita shi ta hanyar yin yawon shakatawa da yin karatu a kasashen ketare da dai sauransu.(Asabe)