Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 16:32:53    
Ministan kasuwanci na kasar Sin ya nuna cewar a cikin watannin masu zuwa za a ci gaba da samun cikas sosai a fannin cinikin kayan shigi da fici na kasar Sin

cri

A gun taron manema labaru da aka shirya a ran 10 ga wata a taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na shekara-shekara da aka saba yi, ministan kasuwanci na kasar Sin Chen Deming ya nuna cewa, bisa wata kididdiga da aka yi, an ce, a cikin watannin masu zuwa za a ci gaba da samun hali mai tsanani a fannin cinikin kayan shigi da fici na kasar Sin.

Bisa kididdiga da aka yi, an ce, tun daga watan Nuwanban bara, yawan kudin da ake samu daga harkokin shigi da fici ya ragu, kuma a watan Janairu, yawan kudin da ake samu daga wannan harka ya ragu da kashi 3 ckin kashi 10. Bisa nazarin da hukumar kwastan ta kasar Sin ta yi, an ce, mai yiyuwa ne yawan kudin da ake samu daga harkokin shigi da fici zai ci gaba da raguwa.

Chen Deming ya nuna cewa, sabo da tattalin arzikin duniya ya ci gaba da samun cikas, da akwai matsaloli da yawa game da harkokin kudi na kasar Amurka da ba su fito fili ba, kuma matsalar kudi da kasashen Turai da kasashen gabashin Turai suke fuskatar tana ci gaba da tabarbarewa, sabo da haka, a cikin watanni masu zuwa za a ci gaba da samun matsanancin hali na cinikin kayan shigi da fici na kasar Sin.

Chen Deming ya nuna cewa, kasar Sin ta tsaida manufofin a fannonin tara kudin haraji da samun kudi da sauransu don warware batun raguwar yawan kudi da ake samu daga harkokin shigi da fici.(Abubakar)