Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 16:15:15    
Kasar Sin ta nuna adawa ga ra'ayin ba da kariya ga cinikayya

cri

A ran 10 ga wata, ministan ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Chen Deming ya jaddada a taron maneman labaru na shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin cewa, kasar Sin ta nuna adawa ga ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, kuma tana son ciyar da shawarwari kan cinikayya tsakanin bangarori daban daban na duniya wato shawarwarin Doha gaba don kawar da batun ba da kariyar cinikayya.

Chen Deming ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna adawa ga ra'ayoyin ba da kariya ga cinikayya da ya saba wa ka'idojin kungiyar ciniki ta duniya ta WTO. Yanzu dai WTO tana yin bincike kan shirye-shiryen sa kaimi ga tattalin arziki da kasa da kasa suka bayar, kuma ana sa lura kan wannan.

Chen Deming ya bayyana cewa, tilas ne a kara hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, da bunkasa cinikayyar duniya bisa ka'idojin da bangarori daban daban suke bi. A lokacin, yana fatan za a ciyar da shawarwarin Doha gaba cikin adalci don inganta cinikayya tsakanin bangarori daban daban na duniya zuwa wani sabon matsayi a gaban rikicin hada-hadar kudi mai tsanani, da kuma farfado da tattalin arziki.(Zainab)