Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-09 21:47:31    
Kasar Sin ta samu karuwar yawan kasafin kudi na tsaron kasa kamar yadda ya kamata

cri
A ranar 9 ga wata a nan birnin Beijing, daraktan kwamitin kula da ayyukan kasafin kudi na kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Gao Qiang ya bayyana cewa, a wannan halin da ake ciki na fuskantar matsalar kudi, kasar Sin ta samu karuwar yawan kasafin kudi na tsarfon kasa ne kamar yadda ya kamata, kada a nuna damuwa kan wannan.

A lokacin da yake amsar tambayoyin 'yan jarida a wannan rana, Mr. Gao Qiang ya nuna cewa, ko da yake yawan kasafin kudi na tsaron kasa na Sin ya karu da kashi 14.9 cikin dari a shekarar 2009, amma jimlar kasafin kudin, da yawan karuwarsa duk sun yi kasa da na kasashen yamma masu ci gaba.

Bayan haka kuma, Mr. Gao Qiang ya kara bayyana cewa, an kara yawan kasafin kudi na tsaron kasa ne domin inganta yadda ake kula da sojoji, kyautata kayayyakin soja da ake yin amfani da su don tinkari matsalolin da bala'un suka haddasa, da kuma ba da horo kan wannan. (Bilkisu)