Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-09 20:42:36    
Wen Jiabao ya jaddada cewa, ya kamata a samar da yanayin kasuwa na yin takara cikin adalci ga tattalin arziki mai zaman kai

cri
A ranar 9 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya halarci taron dudduba rahoton ayyuka na kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kungiyar wakilai ta lardin Zhejiang ta shirya, inda ya jaddada cewa, ya kamata a samar da yanayin kasuwa mai kyau wajen yin takara cikin adalci ga tattalin arziki mai zaman kai.

Mr. Wen Jiabao ya ce, tattalin arziki masu zaman kai wani muhimmin sashe ne na tattalin arzikin kasuwar gurguzu na kasar Sin, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar kudi ta duniya. Ya kamata a kara fahimtar masana'antu masu zaman kansu. Ko masana'antun mallakar kasa, ko masana'ansu masu zaman kansu, idan suna iya kawo albarkar tattalin arziki, da warware matsalar rashin samun aikin yi, to za a nuna goyon baya gare su. Bayan haka kuma, ya kamata a kara kawar da cikas da tsare-tsare iri iri suka haddasa, musamman ma warware matsalar wahalar tattara kudi da matsakaita da kananan kamfanoni ke fuskanta, domin samar da yanayin kasuwa mai kyau na yin takara cikin adalci ga tattalin arziki masu zaman kansu. (Bilkisu)