Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-09 20:35:56    
Majalisar wakilan jama'a ta Sin za ta inganta aikin sa ido kan kudin biliyan 4000

cri

A ranar 9 ga wata, kwamishina kuma mataimakin direkta na kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da kudi na majalisar wakilan jama'a ta Sin Gao Qiang ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, game da shirin bunkasuwar tattalin arzikin kasar, watau na kebe kudin Sin Yuan biliyan 4000 da gwamnatin Sin ta bayar a shekarar bara, majalisar wakilan jama'a za ta inganta aikin sa ido kan wadannan kudade.

Gao Qing ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'a za ta inganta aikin sa ido kan wadannan jarin da gwamnatin ta zuba. Yayin da aka tsara shirin kasafin kudi na wannan shekara, majalisar wakilan jama'a za ta kara sa ido kan yawan jarin da Sin za ta zuba a cikin kasafin kudin kasar, ko su iya biya bukatun jama'a da shirin bunkasuwar tattalin arzikin kasar da zamantakewar al'umma. A sa'i daya kuma, majalisar wakilan jama'a za ta inganta aikin sa ido yayin da take tsara kasafin kudi na kasar, don hana cin hanci da rashawa da almundahana.(Bako)