Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-09 16:38:33    
Wu Bangguo ya nuna cewar majaliasr wakilan jama'ar kasar Sin za ta kara kafa dokoki a fannin zamantakewa a bana

cri

A cikin wani rahoto a kan ayyukan kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da shugaban kwamitin Wu Bangguo ya gabatarwa wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ran 9 ga wata, muhimmin aiki na kafa dokoki na bana shi ne yin kokarin wajen kafa da gyaran muhimman dokoki na tsarin dokokin kasar, da kuma kara kafa dokoki a fannin zamantakewa, sannan da ci gaba da kafa dokoki a fannonin tattalin arziki da siyasa da al'adu.

Kasar Sin ta nuna cewar za ta kafa tsarin dokoki ta hanyar gurguzu da ke da halin musamman kafin shekarar 2010. Wu Bangguo ya nuna cewa, an riga an kafa tsarin dokoki da ke mayar da kundin tsarin mulki a matsayin mafi muhimmanci, da kuma mayar da dokokin da suka shafi hukumomin kula da dokoki a matsayin babban tushe, kana sun kunshi dokokin kasar da dokokin gwamnati da dokoki na kananan hukumomi. Ayyukan kafa dokokin da za a yi a bana su ne kafa dokar inshora da dokar ba da agaji da dokar ikon mallakar ilmi da sauran dokokin, kuma za a gyara dokar biyan diyya ta kasar da dokar kiyaye sirri ta kasar da dokar zabe da sauran dokokin kasar.(Abubakar)