Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-04 21:16:27    
Hu Jintao yana fatan bangarori daban daban su kara imaninsu domin kokarin fita daga mawuyacin hali

cri

A ran 4 ga watan Maris, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana a birnin Beijing, cewar shekarar da ake ciki yanzu muhimmiyar shekara ce ga kokarin neman ci gaban tattalin arziki cikin sauri ba tare da tangarda ba. Sabo da haka, yana fatan bangarori daban daban na duk kasar su tabbatar da imaninsu domin kokarin fita daga mawuyacin hali tare.

A gun wani taron tattaunawa da aka yi, Hu Jintao ya yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a iya samar da isashen abinci da kyautata aikin ba da ilmi a kauyuka da kuma kirkiro motocin da ke amfani da sabon makamashi.

Mr. Hu ya nuna cewa, daukar hakikanin matakai don tabbatar da karuwar tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a tsakanin al'ummar kasar yana da muhimmiyar ma'ana ga kokarin tabbatar da halin da ake ciki a fannonin bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare a cikin gida da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a tsakanin al'umma da raya zaman al'umma mai jituwa daga dukkan fannoni a kasar Sin. (Sanusi Chen)