Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-02 21:49:38    
An yaba wa "takarda kan yadda aka yi gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a Tibet cikin shekaru 50 da suka gabata"

cri
A ran 2 ga wata, madam Dekyi, mataimakiyar shugaban jihar Tibet mai cin gashin kanta ta bayyana a birnin Lhasa, cewar gwamnatin tsakiya ta bayar da "takarda kan yadda aka yi gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a Tibet cikin shekaru 50 da suka gabata" musamman, wannan ya bayyana yadda gwamnatin tsakiya ta jama'a take mai da hankali da kuma kula da jama'ar kabilu daban daban da suke zaune a jihar Tibet, kuma ta bayyana fata bai daya na jama'ar kabilu daban daban na jihar.

Madam Dekyi ta nuna cewa, a cikin wannan takarda mai rufin fari, an yi amfani da dimbin bayanan tarihi domin kwatanta su da hakikanin halin da ake ciki yanzu domin gano mugun tsarin bauta na mulkin kama karya da aka bi kafin a yi gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a Tibet. Kuma an bayyana manyan sauye-sauye da ci gaban da aka samu a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu a jihar a cikin shekaru 50 da suka gabata.

Madam Dekyi ta kara da cewa, idan ba a yi gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet ba, to da jama'ar da yawansu ya kai kashi 95 cikin kashi dari bisa jimillar yawan mutanen jihar ba za su iya samun 'yancin kai ba, kuma jihar Tibet ba za ta iya samun ci gaba kamar yadda aka gani yanzu ba, har ma ikon hakkin dan Adam na jihar Tibet ba zai iya samun kyautatuwa ba. Jama'ar jihar Tibet ma ba za su iya samun kyakkyawan zaman rayuwa ba.

Madam Dekyi ta ce, rukunin Dalai yana son samun koma baya da kuma maido da tsarin bauta a yankin Tibet, jama'ar Tibet ba za su iya amincewa da faruwar haka ba, kuma tabbas ne zai sha kaye. (Sanusi Chen)