Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-25 15:57:17    
(Sabunta)Al'ummar Tibet ta wurare daban daban na murnar bikinsu na sabuwar shekara

cri

Ranar 25 ga wata, rana ce ta farko ta sabuwar shekara ta al'ummar Tibet, al'ummar Tibet ta wurare daban daban da yawansu ya kai miliyan 5 na shirya gaggarumin biki domin maraba da bikinsu na sabuwar shekara.

Bisa al'adun gargajiya na al'ummar Tibet, an ce, a ranar farko ta sabuwar shekara ta safe, dole ne al'ummar Tibet su je deba ruwa mai tsarki da alheri na ganga na farko na sabuwar shekara. A birnin Lhasa watau hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kanta wadda ke da al'ummar Tibet mafiya yawa, da karfe 5 na safe, al'umomin Tibet da ke birnin Lhasa da ma wasu garuruwa da ke kusa da birnin Lhasa, sun je garin Sangmu da ke gundumar Duilongdeqing, domin deba ruwa na ganga na farko na sabuwar shekara, kana kuma a dandalin Longwangtan da ke fadar sarki na Potala na al'ummar Tibet, kungiyar wasan kwaikwayo ta jihar Tibet ta nuna wasanni masu kayatarwa ga 'yan uwansu.

Dadin dadawa kuma, A yankin da aka fi samun al'ummar Tibet mafiya yawa da ke lardin Qinghai a kasar Sin, al'ummar Tibet sun yi nune-nunen tufafinsu a bakin babban tabkin Qinghaihu, kuma an yi kide-kide da raye-raye da dai sauran bukukuwa da dama domin murnar bikinsu na sabuwar shekara. Haka kuma, A yankin al'ummar Tibet na GanZi da yankin al'umomin Tibet da Qiang na Aba da ke lardin Sichuan a kasar Sin, ana iya ganin kyallaye da jajayen fitilu na murnar bikin sabuwar shekara. Kazalika kuma matasa da dama sun yi wasannin wuta domin murnar sabuwar shekara. A yankin al'ummar Tibet da ke birnin Diqing da ke lardin Yunnan na kasar Sin, an yi wake-wake da raye-raye domin bikin murnar sabuwar shekara.

A birnin Beijing, a Yong Hegong watau gidan ibada na Buddhism mafi girma a kasar Sin, da karfe 8 da minti 20, an fara yin bikin addu'o'i kewaye wurin, kuma lalle gaggarumin biki ya jawo hankulan mutane da dama. Haka kuma a jami'ar kananan kabilu ta tsakiya ta kasar Sin, daliban kabilar Tibet sun shirya bikin nune-nunen hotunan da su da kansu suka dauka, don bayyana wa mutane ainihin halin da da jihar Tibet ke ciki. (Bako)