Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-23 16:09:06    
Kayayyakin da aka yi jigila ta hanyar jirgin kasa tsakanin lardin Qinghai da jihar Tibet na kasar Sin sun karu da ton miliyan 5 a kowace shekara

cri
Tun lokacin da aka kaddamar da zirga-zirgar jirgin kasa tsakanin lardin Qinghai da jihar Tibet, kayayyaki da aka yi jigilar ta jiragen kasa sun karu da ton miliyan 5 a kowace shekara, ana sanya ran cewa kayayyakin da za a yi jigila ta hanyar nan zai kai ton miliyan 30.

Manema labarai sun sami bayani daga kamfanin hanyar jirgin kasa tsakanin lardin Qinghai da jihar Tibet cewa, a shekarar bara, an kammala aikin jigilar kayayyakin da yawansu ya kai fiye da ton miliyan 24, wanda ya karu da kashi 25 cikin kashi dari. Yawancin kayayyakin da aka shigar da su a jihar Tibet sun hada da kayayyakin gine gine da abinci da kayayyakin masarufi na zaman yau da kullum, kuma kayayyakin da aka fitar da su daga jihar Tibet sun hada da kayayyakin musamman na jihar da kayayyakin gona da sauransu. Kaddamar da zirga-zirgar hanyar jirgin kasa tsakanin lardin Qinghai da jihar Tibet ta taka mihimmiyar rawa wajen kara kafa manyan ayyuka a jihar Tibet da kyautata halin zaman rayuwar jama'a da na ayyuka.(Fatima)