Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-18 11:04:48    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban jam'iyyar yaki ta Mauritius

cri
A ran 17 ga wata a birnin Port Louis, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban jam'iyyar yaki ta Mauritius Paul Berenger.

Hu Jintao ya bayyana cewa, dalilin da ya sa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta yi ta bunkasa da kyau shi ne dangantakar tana da kyakyawan tushe, kuma bangarorin biyu suna neman moriya daya, kana da su ba da muhimmanci kan dangantakar. Sin ta yi farin ciki da ganin cewa, duk jam'iyyu na kasar Mauritius suna bin manufar nuna zumunci ga Sin, da dukufa kan bunkasa dangantakar dake tsakaninsu. Ya jaddada cewa, Sin ta mai da hankali kan bunkasa abokiyar dangantakar hadin kai dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan yin kokari tare da kasar Mauritius na tinkarar matsalar kudi.

Bugu da kari, Hu Jintao ya yi nuni da cewa, kara mu'amala tsakanin jam'iyyu muhimmin aiki ne wajen bunkasar dangantakar dake tsakaninsu. A nan gaba, jam'iyyar kwaminis ta Sin tana son kara hadin gwiwa da mu'amala da jam'iyyu na Mauritius don ci gaba da samun bunkasuwa a kan dangantakar dake tsakaninsu.

Mr. Paul Berenger yana maraba da ziyarar da Hu Jintao ya yi, da nuna babban yabo ga kasar Sin da ta dauki matakai don tinkarar matsalar kudi da kasa da kasa ke fuskanta, kuma ya nuna godiya ga kasar Sin da ta taka muhimmiyar rawa a Afrika, da taimakon da ta baiwa Mauritius bayan da kafuwar dangantakar diplomasiya dake tsakanin kasashen biyu. Jam'iyyar yaki ta Mauritius tana fatan kara yin mu'amala da jam'iyyar kwaminis ta Sin da tsaya kan bin manufar Sin daya tak.(Asabe)