Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-18 10:41:01    
Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya kammala ziyarar hadin gwiwa da karfafa aminci a kasashen Asiya da Afrika kuma ya dawo nan birnin Beijing

cri
Bayan da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya kammala ziyarar aikinsa a kasashen Saudiyya da Mali da Senegal da Tanzania da Mauritius, a ranar 18 ga wata da safe, ya dawo nan birnin Beijing.

Yayin da ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Yang Jiechi ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, ziyarar aiki da Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi na wannan gami a karkashin sabon halin da ake ciki yanzu, ta kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe masu tasowa, haka kuma ta kara inganta da zurfafa dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Asiya da Afrika, kana kuma ta kara karfafa aminci da ke tsakanin jama'ar Sin da kasashen Asiya da Afrika, lalle wannan ziyara ta sami sakamako mai kyau.

Sakataren ofishin sakatariya na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma direktan ofishin kwamitin tsakiya na Sin Ling Jihua kuma sakataren ofishin sakatariya na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma direktan ofishin yin nazari kan manufofi na kwamitin tsakiya na kasar Sin Wang Huning da wakilan majalisar gudanarwa Daibingguo da 'yan rakiya sun dawo nan birnin Beijing tare.(Bako)